Majalisar Dinkin Duniya Tana Jiamamin Mutuwar Kofi Annan

[ad_1]

Iyalan Annan da gidauniyarsa ne suka sanar da labarin mutuwarsa a cikin wani sakon Twitter, inda suka ce ya mutu cikin kwanciyar hankali bayan wani dan rashin lafiya a yau Asabar.

Sanarwar Twitter ta kwantanta Annan da dattijo na duniya wanda ya himmantu wurin kishin ci gaban kasashen duniya da ya sadaukar da rayuwarsa wurin neman zaman lafiyar duniya. A lokacin aikinsa na jagorancin MDD, ya yi aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya, da aiwatar da shirye shiryen ci gaba da kare hakkokin bil adama da bin tsarin doka da oda.

Ita ma Majalisar Dinkin Duniyar ta aike da wani sakon Twitter a yau, tana jimamin wannan rashin babban mutum, shugaba kuma mai hangen nesa, sakon na cewar kayi rayuwa mai kyau kuma abin koyi.

Kofi Annan haifaffen Ghana, shine bakar fatar Afrikan farko da ya fara derewa a matsayin babban maga takardan MDD daga 1997 zuwa 2006.

Kuma shine babban sakataren majalisar na farko da rike mukamai dabam dabam a matsayin ma’aikacin majalisar.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...