Daga Sabiu Abdullahi
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin da ke tilasta wa gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi su bi hukuncin Kotun Koli game da asusun kananan hukumomi.
Wannan hukunci ya tanadi cewa kudaden da aka ware wa kananan hukumomi su kasance kai tsaye don amfani da su wajen ayyukan da aka kebe musu, wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godwin Akpabio, ya bayyana muhimmancin wannan kudiri a kasa baki daya.
Ya ce, “Mun yarda da cewa Kotun Koli ita ce babbar kotun kasar nan, kuma ba za ta yanke hukunci ba tare da an tabbatar da aiwatar da shi ba.”
Kudirin, wanda Sanata Tony Okechukwu Nwoye ya dauki nauyi, yana nufin dakatar da gwamnatocin jihohi daga kafa dokokin da ke tauye ‘yancin kananan hukumomi, kamar yadda Sashe na 7 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.