Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da N1.15 Tiriliyan Da Tinubu Ya Nemi A Ranto

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar rance na N1.15 tiriliyan daga kasuwar bashin cikin gida domin cike gibi a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Amincewar ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan bashin cikin gida da na ƙasashen waje ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Laraba.

Rahoton ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 ya kai N59.99 tiriliyan, wanda ya fi abin da fadar shugaban ƙasa ta gabatar da N5.25 tiriliyan. Wannan ya haifar da gibin kasafi na N14.10 tiriliyan, inda aka riga aka amince da N12.95 tiriliyan don aro, sai kuma saura N1.15 tiriliyan da aka amince da shi yanzu.

Haka kuma, majalisa ta amince da ƙudurin Sanata Abdul Ningi wanda ke umartar kwamitin kasafin kuɗi da ya ƙara sa ido kan yadda za a yi amfani da kuɗaɗen da aka aro, domin tabbatar da cewa an kashe su bisa manufa a cikin shekarar kuɗi ta 2025.

A ranar 4 ga Nuwamba, Shugaba Tinubu ya aika da wasiƙa zuwa majalisar dokoki domin neman amincewa da sabon bashi na N1.15 tiriliyan daga kasuwar bashin cikin gida, da nufin rufe gibin kuɗi da tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata a kasafin shekarar 2025.

More from this stream

Recomended