
Majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tura karin dakarun soja zuwa jihar Benue biyo bayan harin da yan bindiga suka kai garin Yelewata dake karamar hukumar Guma ta jihar.
Majalisar ta yanke daukar matakin ne biyo bayan kudirin da Titus Zam sanata mai wakiltar mazabar Benue maso yamma a majalisar dattawa ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.
Zam ya bayyana harin da “Kisan gilla marar misaltuwa,” da wasu yan ta’adda su ka yi.
Dan majalisar ya jaddada bukatar dake akwai na gwamnatin tarayya ta tura karin dakarun soja zuwa garin Yelewata da kuma sauran garuruwan da abun ya shafa a jihar Benue domin dawo da doka da oda.
Ya ce harin da aka kai kan fararen hula da suka hada da yara da mata an kai shi ne da mugunta.
Da yake tsokaci kan batun, Sanata Abdul Ningi ya ce harin zallar ta’addanci ne kuma bai kamata a kyale maharan da yawansu ya kai 200 su yi batan dabo bayan kai harin sai kace wasu mala’iku.
Da yake yabawa Tinubu kan ziyarar da ya kai jihar Benue, Ningi ya ce kamata ya yi Tinubu yaje Yelewata da kansa.
Barau Jibrin mataimakin shugaban majalisar ya yi kira da a kara bawa jami’an tsaro hadin kai domin su kamo wadanda suka aikata laifin.
Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gyara gidajen da suka lalace ta biya diya ga wadanda suka jikkata kana ta kara tsaurara matakan tsaro.