Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin kwamishinonin zabe biyar

Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Laraba ta amince da nadin kwamishinonin zabe biyar na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC.

Amincewa da nadin kwamishinonin na zuwa ne biyo bayan dubawa tare da  amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan hukumar INEC.

Wadanda aka tabbatar da su sun hada da Umar Yusuf Garba (Kano), Sa’ad Umar Idris (Bauchi), Chukwuemeka Ibeziako (Anambra), Umar Mukhtar (Borno), da kuma  DrJohnson Alalibo Sinikiem (Bayelsa).

Kowane kwamishinan zabe ana sa ran zai shafe shekaru biyar akan mukaminsa.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya mikawa majalisar Dattawan sunayen mutanen  a cikin wata wasika da ya aike da ita majalisar a ranar 18 ga watan Maris.

More from this stream

Recomended