Majalisar Dattawa Ta Hana Daukar Ƴan Ƙasa Da Shekara 18 Aikin Soja

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da ke hana ɗaukar mutanen da ba su kai shekara 18 ba a rundunar sojojin ƙasar. Wannan mataki ya zo ne bayan ta karanta dokar Armed Forces (Repeal and Re-enactment) Bill, 2025 karo na biyu a zauren majalisar.

Dokar na da nufin tabbatar da cewa tsarin ɗaukar ma’aikata a rundunar soji ya yi daidai da tanadin dokar Child Rights Act, 2003, da yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haƙƙin yara, da kuma African Charter on the Rights and Welfare of the Child.

Sanata Abdulaziz Yar’Adua daga Katsina ta Tsakiya ne ya gabatar da kudirin. Yace dokar sojan yanzu ta tsufa domin an samo ta ne daga tsohuwar doka ta mulkin soja wadda ba ta dace da tsarin dimokuraɗiyya da zamani ba.

Kudirin ya kuma ƙunshi sabbin gyare-gyare da suka haɗa da faɗaɗa ma’anar manyan laifukan soja, da samar da hukunci masu dacewa, tare da kare ‘yancin kotunan soja daga tsoma bakin manyan jami’ai, domin hana amfani da iko ta hanyar da ta sabawa doka.

More from this stream

Recomended