Majalisar dattawa ta fara yunkurin kawo karshen amfani da motoci masu aiki da fetur

Majalisar dattawa ta fara ƙoƙarin kawo karshen yin amfani da motoci masu aiki da man fetur inda ta fara nazartar kudirin dokar motoci masu amfani da wutar lantarki.

Dokar da majalisar za ta samar kan yadda za a samar da dokoki da kuma tsarin jadawalin yadda Najeriya za ta sauya daga kasa mai amfani da motoci dake amfani da fetur ya zuwa masu amfani da wutar lantarki ya tsallake karatu na biyu a majalisar.

Sanata Orji Uzor Kalu wanda ya samar da kudirin dokar ya ce an gabatar da ita ne domin rage hayaki mai gurbata muhalli, bunkasa masana’antu da kuma dora na Najeriya a wani matsayi da za ta amfana  kan yadda duniya ke juyawa ya zuwa ababen hawa marasa gurɓata ya na yi

Kalu wanda ya ce ɓangaren sufuri shi ne yake samar da kaso 30 cikin 100 na iskar da gurɓata yanayi a Najeriya ya kara da cewa Najeriya na fuskantar zama koma baya duba da yadda wasu ƙasashen Afrika su ka yi nisa wajen amfani da ababen hawa masu amfani da lantarki.

More from this stream

Recomended