Majalisar dattawa ta dage zamanta na yau

Majalisar dattawa ta dage zamanta na ranar Talata saboda karancin halartar yan majalisar.

Philip Tanimu Aduda,sanata mai wakiltar birnin tarayya Abuja shine ya gabatar da kudurin dage zaman majalisar bisa dogaro da sashi na 10(3) da ya ce yan majalisar baza su zauna ba matsawar suka gaza kaiwa mafi ƙarancin wakilan da doka ta tanada.

Sanatoci 38 ake bukata kafin majalisar ta zauna ta tattauna kan wani batu.

Aduda ya bayyana cewa majalisar ta kasance babu sanatoci saboda yawancin su suna sassa daban daban na kasar na suna duba ayyuka.

Sanatoci kasa da 20 ne dai suka halarci zaman na yau.

More from this stream

Recomended