Majalisar dattawa ta amince Tinubu ya ciwo bashin dala biliyan $2.2

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ta cin bashin dalar Amurka biliyan $2.2.

Majalisar dattawan ta amince da buƙatar  ciwon  bashin ne bayan da ta karbi rahoton, Sanata Aliyu Wamakko shugaban kwamitin majalisar kan basukan cikin gida da kuma na ƙasashen waje.

Adadin kuɗin ya kama naira tiriliyan ₦1.7 idan akayi amfani da ₦800 kan kowace $1 a kasuwar musayar kuɗaɗe kuma za ayi amfani da kuɗin ne wajen cike giɓin naira tiriliyan 9.1 dake cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.

A lokacin da yake gabatar da rahoton Wamakko ya ce za a samu kuɗin ne ta hanyar takardar lamuni ta Eurobond da kuma takardar lamuni ta kasuwanci musulunci wato Sukuk.

A ranar Talata ne shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu ya nemi majalisar ta amince masa ya ciwo bashin.

More from this stream

Recomended