Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Laftana Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa

Majalisar dattawa ta amince da naɗin Laftana Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya.

Amincewar ta biyo bayan nazarin rahoton kwamitin harkokin rundunar soji na majalisar, wanda Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ke shugabanta.

Majalisar ta amince da shawarwarin da kwamitin ya gabatar cikin rahoton, ba tare da wata gardama ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Laftana Janar Oluyede a matsayin mai riƙon mukamin babban hafsan sojin ƙasa, bayan rashin lafiya da kuma rasuwar wanda ya riƙe mukamin a baya, Laftana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.

More from this stream

Recomended