A cigaban zaman da take na kada kuri’a kan rahoton kwamitin majalisar dattawa na gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 an gabatar da kudurin sauyawa wasu kananan hukumomi sunana.
Majalisar ta amince da kudurin na sauyawa kananan hukumomin suna sai dai taki amincewa da sauya sunan karamar hukuma guda daga cikin jerin sunayen da aka gabatar.
A cikin gyaran da aka yi an sauya sunan karamar hukumar Kunchi dake jihar Kano zuwa karamar hukumar Ghari.
Akwai kananan hukumomin Afikpo South da Afikpo North a jihar Ebonyi inda a yanzu suka koma Afikpo da kuma Edda.
Sauran sun hada da Egbado North da Egbado south a jihar Ogun inda a yanzu suka koma Yewa North da kuma Yewa South.
Har ila yau majalisar ta amince da gyaran sunayen wasu kananan hukumomin ciki har da Atigbo a jihar Oyo inda ta koma sunan Atisbo.
Majalisar kuma yi watsi da kudurin sauya sunan karamar hukumar Barikin Ladi zuwa Gwol a jihar Filato abin da ya fusata sanata Istifanus Gyang daga jihar inda ya zargi sanatocin da suka fito daga jihohin arewa da kada kuri’ar amincewa da kudurin.