Mai satar mota a Najeriya ya kai Nijar ya faɗa hannun ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wani mai suna Mubarak Kabiru da yake sayar da motocin da aka sata a Najeriya a jamhuriyar Nijar.

A wata sanarwa ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ta Kaduna, Mansur Hassan ya ce an kama Mubarak ne bayan da wani mutumin kirki ya cunawa ƴan sanda shi ranar 27 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 06:30 na yamma.

” Wani mutum ya kai rahoton cewa an nemi taimakonsa wajen karɓo mota ƙirar Lexus LX 470 daga wurin mai gyara,” a cewar sanarwar.

Hassan ya ce mutumin kirkin ya yi zargin cewa motar ta sata ce shi ne ya kai rahoton ofishin ƴan sanda na Magaji Gari dake Kaduna.

Binciken da aka yi yasa aka gano takardun motar aka kuma kira mai motar inda ya ce wasu mutane biyar ne suka yi amfani da bindiga wajen ƙwace masa motarsa a gidansa dake Utako a Abuja.

Binciken ɗakin wanda aka kama da aka yi a wani hotal dake Kaduna an gano na’urar kashe network da zai hana a bi sawun motar.

Wanda aka kama ɗin ya ce yana yiwa wani mutum mai suna Daud  a jamhuriyar Nijar shi ya ke yiwa aiki.

More from this stream

Recomended