Mai Mala Buni: Ya kamata a yi maraba da miƙa-wuyan mayaƙan Boko Haram maimakon yanke ƙauna

Gwamnan jihar Yobe Maumala Buni

Gwamnan jihar Yobe da ke arewa maos yammacin Najeriya Alhaji Mai Mala Buni ya yi kira ga al`umma da ta yi maraba da miƙa-wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi, maimakon yanke-ƙauna da wasu ke yi gama da sahihancin tubarsu.

A hirar da ya yi da sashen Hausa na BBC, gwamnan ya ce babu yakin da ya ƙare ba tare da hawa teburin sulhu ba, saboda haka Allah ne ya karɓi addu’ar da jama’a ke yi, har mayaƙan suka fara jefar da bindigoginsu suna tuba.

“Ina duba misali da yadda a da Boko Haram suke cikin birnin Maiduguri, sai Allah cikin ikonsa ‘ yan ƙato da gora ne suka koresu daga Maiduguri suka fita.

“Kuma wannan ma ya ishe mu aya mu gane cewa Allah yana yin abin da ya ga dama, lokacin da ya ga dama,” in ji gwamnan.

Ya ce fatansa shi ne Allah ya sa wannan tuba ya zama da gaske ne kuma ya yi kira ga mutane da su ci gaba da addu’a.

Sai dai wasu sun riƙa sukar yadda ‘yan Boko Haram ke miƙa wuya saboda a cewarsu akwai wasu a baya da suka yi irin haka, kuma ya kasance tubar mazuru ce suka yi. A kan haka suke ganin wannan karon ma ba lalle ne abin ya ɗore ba.

Amma a cewar gwamnan jihar Yobe ya kamata a bar maganar a hannun jamian tsaro.

Ya ƙara da cewa akwai tsarin da ake bi ake karɓar tuban.

Sai dai ya yi kira ga jami’an tsaro a kan kada su yi sakaci a aikinsu.

Kawo yanzu kimanin mayaƙan Boko Haram da iyalansu su 6000 suka yi saranda.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...