Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 93.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya tabbatar da rasuwar tata a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar Mohammed, za a yi jana’izar marigayiyar da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a yau Lahadi a garin Radda da ke Jihar Katsina.
Mataimakin gwamnan ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai ƙarfi da ɗaukakar girma, wadda hikimarta ta samo asali daga dogon tarihin rayuwa.
Mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Radda, Ta Rasu Tana Da Shekaru 93
