Mahaifiya da ƴar uwar  gwamnan Taraba sun tsallake rijiya da baya

Atsi Kefas ƴar uwar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ta samu raunin harbin bindiga bayan da ɗan sandan da yake basu kariya ya harbe ta bisa kuskure a lokacin da suke musayar wuta da ƴan bindiga.

Lamarin ya faru ne akan titin Kente dake karamar hukumar Wukari ta jihar lokacin da mahaifiyar gwamnan Jummai tare da Atsi ke tafiya a cikin mota.

A cewar wasu rahotanni maharan sun kai farmaki kan motar da mahaifiyar gwamnan ke ciki.

Biyo bayan harin dakarun soja sun yi gaggawar ɗauke Jummai da Atsi a cikin jirgi mai saukar ungulu na ɗaukar marasa lafiya daga wurin da aka kai harin.

An garzaya da ƴar uwar gwamnan ya zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci kuma kawo yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar kan halin da take ciki.

More from this stream

Recomended