Mahaifi ya fille kan ɗiyarsa don yin asiri

Jami’an tsaro na jihar Edo sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Ovwarueso bisa zarginsa da fille kan diyarsa bisa zarginta da laifin kashe kudi a garin Benin na jihar Edo.

An kama wanda ake zargin ne a Uteh, Upper Mission, inda yake zaune a ranar Alhamis din da ta gabata da misalin tsakar dare tare da kam marigayiyar a cikin wata leda

An ce ya aikata wannan mummunan aiki, sai da ya daure matarsa inda ya aiwatar da kisan a gabanta.

Matarsa, wacce ba a bayyana sunanta ba a lokacin da aka buga wannan rahoton, ta ce, “Halin mijina ya canza kwanan nan.  Ya ci gaba da cewa kada in kara kallonsa a matsayin talaka.

“A wurin aikinsa yana siya wa kowa abin sha kamar yana bikin. Hatta abokan aikinsa sun yi mamakin sabon salon kashe kudinsa. 

“Har ya ce musu kudinsa na kusa.  Ba mu taba sanin yana da shirin yin amfani da ’yarmu wajen yin asiri ba.”

More News

Za a rataye wanda ya ɗaba wa wani wuƙa har lahira

An yanke wani mutum mai suna Hamza Mohammed  hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ya daba wa wani mutum wuka har lahira a...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji sun kashe kwamandojin ƴan ta’adda a Najeriya

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce bangarenta na rundunar Operation Hadin Kai a ranar 10 ga watan Janairu ya kawar da wasu manyan kwamandojin...

Wani ya kashe abokinsa saboda kuɗin farantin abinci

Wani mutum mai suna John ya rasa ransa bayan abokinsa, Akinola Adeleye, ya caka masa wuka har lahira a kan takaddamar wanda zai biya...