Magoya bayan jam’iyar PDP sun gudanar da zanga-zanga a jihar Edo

Magoya bayan jam’iyar PDP a jihar Edo sun gudanar da zanga-zanga ranar Lahadi a Benin babban birnin jihar kan yadda ake cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar.

Zanga-zangar ta gudana ne a kusa da ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC dake  jihar inda ake cigaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Ya zuwa maraicen ranar Lahadi jam’iyar APC ce ke kan gaba bayan da ta lashe zaɓen a ƙananan hukumomi 11 cikin 16 da aka bayyana sakamakonsu.

Tun da farko wasu mambobin jam’iyar ta PDP sun tattaru a bakin ofishin hukumar ta INEC inda suke zargin cewa ana shirin sauya sakamakon zaɓen.

Jami’an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa.

More from this stream

Recomended