Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam’iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam’iyar na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso inda suka riƙa ƙona jar hula alamar tafiyar dariƙar Kwankwasiya.

Shugaban tsagin jam’iyar na ƙasa, Dr. Gilbert Agbo wanda ya jagoranci  gangamin adawa da Kwankwasiya a ofishin jam’iyar  dake Minna a jihar Niger ya ce Kwankwaso da ƴan Kwankwasiya  barazana ne ga cigaban jam’iyar NNPP dama cigaba da wanzuwarta a matsayin jam’iya.

Rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyar NNPP na kawo damuwa kan haɗin kan jam’iyar dama makomarta anan gaba.

A yayin da rikicin ke cigaba da fitowa fili mutane da dama sun zuba idanu su ga yadda za a kaya.

Da yake magana a wurin taron shiya  na jam’iyar a Minna, Dr. Agbo ya ce dakatarwar da kwamitin gudanarwar jam’iyar ya yiwa Kwankwaso a taron jam’iyar na Lagos na nufin cewa an kori Kwankwaso daga jam’iyar ta NNPP.

Ya ƙara da cewa ana sa ran  gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyar.

Amma da yake mayar da martani, Mallam Danladi Umar Abdulhamid shugaban kungiyar Kwankwasiya a jihar Niger ya ce shugabancin Dr. Agbo haramtacce ne kuma Kwankwaso ne jagoran jam’iyar NNPP a Najeriya ƙarƙashin, Ahmad Ajuji shugaban jam’iyar na ƙasa.

More from this stream

Recomended