Magoya bayan Ambode sun gudanar da zanga-zangar lumana

Magoya bayan gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode sun gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna goyonsu kan takarar gwamnan a karo na biyu.

Masu zanga-zanga sun dage kan cewa dole ne jam’iyar APC ta bawa kowanne dan takara dama a zaben fidda gwanin gwamnan da za a gudanar ranar Litinin.

Magoya bayan gwamnan sun yi jerin gwano tun daga Maryland ya zuwa Freedom Park dake Ojota.

Takarar gwamna Ambode a karo na biyu na fuskantar adawa daga wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar da suke zargin gwamnan ya yi watsi da su.

Tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jagoran jam’iyar APC na kasa, Bola Ahmad Tinubu na daga cikin na gaba-gaba wajen nuna adawa da takarar gwamnan.

More from this stream

Recomended