Mafita Dangane Da Bangar Siyasa A Najeriya, Daga Lawan M. Ahmad Karaye

Shigowar shekarar 2019 tamkar an buga gangar siyasa ne ko ince an bude wani sabon shafin cigaba da k’addamarda manufofi da ‘yan siyasa keyi domin tunkarar zab’ukan shekarar 2019.

Hakika lokaci yayi da dukkan al’umma tagari zata zabure wajen jan kunnen matasa musamman masu yin bangar siyasa alokutan gudanarda yakin neman zabe da kuma lokacin zabe. Lokaci ne daya kamata malamai da iyayen yara, sarakuna, kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki su fad’akar da matasa illar bangar siyasa da irin hatsarin da ke cikinta kuma tareda nuna masu lokaci yayi daza’a daina siyasa cikin duhu, murike sana’ar mu hannu bibiyu.
Allah ya jikan Malam Aminu kano yana cewa “karike sana’arka da hannun dama kakuma rike siyasar ka da hannun hagu” Anan bai nuna siyasa bata da muhimmanci ba saidai sana’oin dogaro dakai sunfi siyasar muhimmanci.

Akwai hanyoyi da dama da za’a iya magance ko kawo raguwar bangar siyasa a wannan kasa:

-Abu na farko ‘yan siyasarmu suji tsoron Allah su kula da tarbiyyar matasa ta hanyar daina basu makamai da miyagun kwayoyi domin yin amfani dasu wajen yin ta’addanci. -Na biyu Akwai bukatar sarakuna waɗanda su ne iyayen al’umma su tsawatar da dukkanin ɓangarorin ƴan siyasa akan bukatar haramta shigo da ‘yan banga ko daba harkokin yakin neman zaɓe.
-Na uku Malaman addini nauyi ne akan su jan hankali da tunatarwa ga al’umma su guji shiga rigingimun siyasa.
-Na hudu kungiyoyin masu kare hakkin ɗan adam da kungiyoyin matasa dole su shigo ciki domin wayar da kan al’umma akan hatsarin shiga fitintinun zaɓe ga matasa.
-Na biyar, jami’an tsaro suyi aiki tuk’uru kuma tsakani da Allah domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tareda nuna b’angaranci ko sonkai ba.
– Hukumar zaɓe ta kasa wato INEC dole su tsaya akan gaskiya da adalci, wajen gudanar da zaɓe da wajen bayyana sakamakon don gudun rikici.
-Dole ‘yan siyasa su tsawatar da magoya bayansu cewar harkar siyasa ba ta a ‘mutu ko a yi rai’ ba ce wannan shine zai tabbatarma al’umma dominsu akeyi badon wata manufaba.

A karshe ina mai kara kira ga matasa da muyi karatun ta nutsu mu duba matsayi da halinda kasarmu ke ciki muyi duba izuwa ga shugaban da muke ganin zai iya fitar damu daga halinda kasarmu ke ciki.

Muna addu’ar Allah ya zaunar da kasarmu lafiya ya azurtamu da shugabanni nagari masu kishin kasarmu wadanda zasu sama sanadin gyaruwar kasarmu koda bama sonsu.

Lawan M. Ahmad Karaye ne ya rubuto wannan maqala daga Kano kuma za a iya samunsa a shafinsa na Facebook: Lawan M. Ahmad Karaye.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...