Ma’aikatan jihar Nasarawa sun janye yajin aikin da su ke

Mambobin kungiyar ƙwadago ta NLC da TUC a jihar Nasarawa sun janye yajin aikin da suka tsunduma a ciki kan kin aiwatar da fara biyan mafi ƙarancin albashi a jihar.

Da yake magana da manema labarai a wurin wani taron ƴan jaridu ranar Litinin a lafiya babban birnin jihar,  Ismaila Okoh shugaban kungiyar NLC a jihar Nasarawa ya ce ma’aikatan sun janye  yajin aikin bayan wata doguwar tattaunawa da gwamnati da kuma tsoma baki da wasu masu ruwa da tsaki suka yi.

A ranar 23 ga watan Disamba kungiyar ta NLC ta ce ba bu sauyi kan wa’adin ranar 1 ga watan Disamba da ta bawa  gwamnatocin jihohi da su aiwatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Okoh ya ce ma’aikatan sun janye yajin aikin ne bayan da gwamnatin jihar Nasarawa ta amince ta yi sabon ƙarin albashin.

More from this stream

Recomended