
Kungiyar ƙwadago ta NLC reshen birnin tarayya Abuja ta umarci ma’aikatan dake kananan hukumomin 6 da su fara yajin aiki tun daga ranar 1 ga watan Disamba.
Knabanyi Adalo shugaban kungiyar shi ne ya bada umarnin a wata sanarwa da ya fitar.
Adalo ya ce an bada umarnin fara yajin aikin ne domin bin matakin sanarwar bayan taron da aka fitar a taron da shugabancin kungiyar NLC na ƙasa ya gudanar a Fatakwal ranar 8 ga watan Nuwamba.
Shugabancin kungiyar ya roki shugabannin ƙananan hukumomin da su fara aiwatar da fara biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Adalo ya ce shugabannin ƙananan hukumomin sun gaza amsa buƙatar da aka gabatar musu ta aiwatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin.