Wasu ma’aikata su 10 a Kenya sun shigar da karar kamfanin Unilever na Burtaniya da Holland a gaban kotun koli da ke London, akan gaza daukan nauyin da ya rataya a wuyansa na kare hakkin dan adam a rikicin bayan zaben shekara ta 2007.
Ma’aikatan sun ce kamfanin ya nuna halin ko-in-kulla wajen kare rayukansu a lokacin, zargin da Unilever ya musanta.
Sama da mutum dubu 1 aka kashe a rikicin.
A lokacin shigar da karar ma’aikatan sun ce akwai masu yiwa kamfanin aiki su 7 cikin wadanda aka kashe, sannan an aikata fyade akan mata 56.
Wakilin BBC ya ce ma’aikatan sun ce shugabanin gudanarwar kamfanin a Kenya sun jefa rayuwarsu a cikin hatsarin barazanar mutuwar bayan ma’aikatan sun shigar da korafinsu.
Sai dai Unilever ya ce ya bai wa ma’aikatansa duk wani taimako da suke bukata a wannan lokaci.