Liverpool ba ta bukatar Coutinho, Neymar ya so zuwa Chelsea

Philippe Coutinho

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Philippe Coutinho

Liverpool ta shaida wa dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, wanda yake zaman aro a Bayern Munich, cewa ba za ta sake sayo shi ba, lokacin da dan wasan na Brazil mai shekara 27 ya tunkari kungiyar da niyyar tattaunawa kan yiwuwar sake komawarsa can.(Mirror)

Arsenal ta janye daga tattaunawar da take yi da zummar sabunta kwangilar dan wasan Gabon mai shekara 30, Pierre-Emerick Aubameyang. An dade ana hasashen cewa dan wasan zai bar Emirates Stadium, inda aka ce Manchester United, Inter Milan, Barcelona, Real Madrid da kuma Chelsea duk suna son dauko shi. (Mirror)

Golan Manchester United dan kasar Spaniniya David de Gea ya ce yana son ci gaba da murza leda a Old Trafford zuwa “shekaru da dama” ko da yake dan wasan mai shekara 29 yana fuskantar barazana a kwace matsayinsa domin bai wa golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 23, wanda yake zaman aro a Sheffield United. (Mail)

Tsohon wakilin Neymar, Wagner Ribiero, ya ce dan wasan na Paris St-Germain dan kasar Brazil, mai shekara 28, ya so komawa Chelsea lokacin yana da shekara 17 a duniya. (Mail)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya “rarrashi” dan wasan Paris St-Germain da Belgium Thomas Meunier domin ya koma can a bazara, ko da yake har yanzu dan wasan mai shekara 28 yana fatan zai sabunta kwangilarsa a Parc des Princes. (L’Equipe, via Teamtalk)

Kocin Chelsea Frank Lampard ya yi magana da dan wasan Napoli Dries Mertens inda yake fatan karbo aron dan wasan dan kasar Belgium mai shekara 32. (Mail)

Dan wasan Netherlands Jetro Willems, mai shekara 26, ya ce yana son komawa Newcastle dindindin bayan da ya kwashe farkon kakar wasan bana yana zaman aro a can daga Eintracht Frankfurt kafin ya ji rauni. (Goal)

Chelsea ta fuskanci koma-baya a kokarinta na dauko golan Ajax Andre Onana domin kuwa dan wasan na Kamaru mai shekara 24 ya shirya tsaf don komawa Barcelona. (Express)

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...