Likitoci za su sake shiga yajin aiki ranar 12 ga wata Janairu

Kungiyar NARD ta  Likitoci Masu Neman Kwarewa ta sanar da shirin sake komawa yajin aiki a ranar 12 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da aka fitar bayan taron gaggawa na shugabannin kungiyar na kasa da ya gudana a ranar 2 ga watan Janairu kungiyar ta ce ta dauki matakin a matsayin martani na gazawar gwamnati na shawo kan batun  walwala da kuma shawo kan wasu matsalolin aiki na likitocin.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun, Muhammad Suleiman shugaban kungiyar na kasa, shugabancin kungiyar na kasa ya ce yajin aikin zai fara da karfe 12:00 na daren ranar Litinin 12 ga watan Janairu.

A wani bangare na shirye-shiryen fara yajin aikin shugabancin kungiyar ya umarci reshen kungiyar na cibiyoyin lafiya guda 91 da suka kira taro tare da fitar da sanarwar bayan taro domin jawo hankalin jama’a kan bukatun kungiyar.

More from this stream

Recomended