Leicester City 0-2 Arsenal: ‘Yan wasan Arteta sun riƙe wuta bayan doke Leicester City

Emile Smith Rowe scores for Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Arsenal ta buga wasa bakwai kenan a Premier ba a doke ta ba

Arsenal ta ci gaba da ƙoƙarinta na baya-bayan nan a gasar Premier League bayan ta doke Leicester City har gida a wasan mako na 10.

‘Yan wasan na Mikel Arteta sun yi amfani da damar da suka samu daga rashin azamar da masu masaukin baƙin suka nuna a farkon wasa.

Hakan ya sa sun samu nasarar cin ƙwallo biyu a minti 20 na farkon wasan, kuma nasarar ita ce wasa na bakwai da Arsenal ta buga ba tare da an doke ta ba.

Gabriel ne ya fara ci wa Arsenal ƙwallo bayan ya saka wa ƙwallon da Saka ya bugo kai daga bugun kwana.

Sai kuma Emile Smith Rowe, wanda ya ɗaɗa ƙwallo a raga sakamakon aikin ƙwarewa da Saka da Lacazette suka aiwatar.

Mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale, ya tare ƙwallaye da dama yayin da ‘yan wasan baya ma suka yi bajintar tsare gida.

Wannan nasarar ta sa ƙungiyar ta Gunners ta tsallako daga mataki na 10 zuwa na 5 a teburin Premier, inda suke matsayi ɗaya da West Ham kafin ta buga wasanta na Lahadi.

(BBCHAUSA)

More from this stream

Recomended