Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huɗu domin ya nemo mutumin da yake karewa.
Mohammed ya ƙara da cewa har yanzu ba a san inda tsohon gwamnan ya shiga ba.
Da yake wa ƴan jaridu jawabi bayan zaman kotun na ranar da alƙali ya jaddada cewa dole ne a kamo wanda yake karewa Mohammed ya ce Bello ya damu sosai kan tsaron lafiyarsa.
“Ya mai girma ma shari’a wannan batu ne da ya shafi ƴan cin yin rayuwa da yake da shi. idan mutum yana da kwarƙwarar damuwa akan barazana ga rayuwarsa ya kamata a lura da haka,” a cewar lauyan cikin buƙatar da ya miƙawa kotun da ta nemi a janye umarni kama Yahaya Bello.
Da yake wa babban lauyan jawabi alƙalin kotun ya ce ” Kai a matsayinka na lauyansa ya kamata ka bashi shawarar data dace. shin shi ka ɗai ne tsohon gwamnan da EFCC ta gayyata ko ta gurfanar a gaban kotu.?”
Ya cigaba da tambayar cewa mutum nawa ne suka mutu a hannu EFCC ya ƙara da cewa idan wani abu ya same shi bayan ya miƙa kansa to dole a tuhumi hukumar ta EFCC da laifi.