Lampard ya kara samun cikas | BBC Sport

Lampard

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelsea ta tashi kunnen doki 1-1 da Leicester City a wasan mako na biyu a gasar cin kofin Premier da suka buga ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Chelsea ce ta fara cin kwallo ta hannun Mason Mount minti bakwai da fara tamaula kuma haka aka ta fi hutu Chelsea tana da ci daya.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Leicester City ta kara matsa kaimi har sai da ta farke kwallon ta hannun Wilfred Ndidi.

Kuma daman shi Ndidi ne ya yi kuskuren da aka karbe kwallo daga kafarsa aka kuma zura a ragar Leicester City.

Da wannan sakamakon Chelsea tana da maki daya a wasa biyu da ta buga, bayan da Manchester United ta fara doke ta da ci 4-0 a makon farko a Old Trafford.

Ita kuwa Leicester City tana da maki biyu, bayan da ta tashi babu ci a wasan makon farko da ta karbi bakuncin Wolverhampton.

A makon jiya ne Liverpool ta yi nasara a kan Chelsea a Uefa Super Cup, inda aka doke kungiyar ta Stamford Bridge a bugun fenariti da ci 5-4, bayan da suka tashi wasa 2-2.

Frank Lampard tsohon dan kwallon Chelsea ya karbi aikin horar da kungiyar a bana, bayan da Maurizio Sarri ya koma Juventus.

Shi kuwa Lampard daga Derby County wadda ya kai wasannin cike gurbin shiga Premier a karon farko da ya ja ragamar kungiyar ya koma aikin jan ragamar Chelsea.

More from this stream

Recomended