
Ministan ƙwadago da kuma ayyukan yi, Simon Lalong ya karɓi shedar cin zaɓensa a matsayinsa na Sanata mai wakiltar mazabar Kudancin Filato a majalisar dattawa.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ayyana ɗan takarar jam’iyar PDP, Napoleon Bali a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan.
Rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen ya saka Lalong ya garzaya kotu wacce kuma ta bashi nasara.
Da yake yanke hukunci jagoran rukunin alkalan kotun uku, mai shari’a Mahmud Tukur ya ce kuri’ar da ɗan takarar jam’iyar PDP ya samu ba halastattu bane saboda an tsayar da shi takara ba bisa ka’ida ba.
Hukuncin ya ce har ya zuwa lokacin da aka gudanar da zaɓe jam’iyar PDP bata da shuganci a jihar.
Bali ya yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaɓen inda ya daukaka kara.
A hukuncin da mai shari’a, Elfaida William Dawodu ya yanke kotun ɗaukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaɓen da ya soke kuri’ar da jam’iyar PDP ta samu a zaɓen.