Wani dan Najeriya mai suna Adedeji Odulesi ya kware a harsunan Ingilishi da Pidgin da Yoruba da Igbo da Hausa da Faransanci da Jamusanci da Sifaniyanci da kuma harshensa na asali wato Ijebu.
An haife shi ne a gidan mai da ’yan’uwa biyar, ciki har da mahaifiyarsa da mahaifinsa, wadanda dukansu ’yan kabilar ljebu ne.
A yankin Warri na jihar Delta, inda aka haife shi a shekarar 1972, Adedeji ya koyi harsunan Yarbanci, Turanci, da Pidgin.
Ya koyi harshen Hausa ne bayan da iyayensa suka koma Sakkwato a shekarar 1981. Iyalinsa sun koma Imo a karshen shekarun 1990, inda ya koyi yaren Igbo.
Ya kuma bayyana cewa ya auri Bafaranshiyar Bayerabiya kuma ya koyar da kansa Jamusanci, Sifaniyanci da Faransanci a Najeriya.
Adedeji ya shawarci iyaye da su yi magana da ’ya’yansu cikin yarensu.