La Liga: ‘Yan wasan Real Madrid da za su je Real Sociedad

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Sociedad za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 30 a gasar La Liga da za su fafata ranar Lahadi.

Tuni kocin Real Madrid, Znedine Zidane ya bayyana ‘yan kwallon da zai je da su Reale Arena domin fuskantar Sociedad.

Messi ya ci kwallo na 699 a karawa da Leganes

Za a kammala Champions da Europa League cikin watan Agusta

Wasab farko da suka kara a gasar La Liga ranar 23 ga watan Satumba Real ce ta yi nasara a gida da ci 3-1.

Wadanda suka ci wa Madrid kwallayen sun hada da Karim Benzema da Fede Valverde da kuma Luka Modric

Ita kuwa Sociedad ta zare kwallo daya ta hannun Willian Jose wanda shi ne ya fara cin kwallo a wasan minti biyu da take leda.

Real Madrid tana ta biyu a kan teburin La Liga, amma idan za ta ci kwallo 4-0 a wasan na Lahadi to za ta koma ta daya.

Barcelona tana ta daya da maki 65 da rarar kwallo 38, Real kuwa tana da maki 62 da rarar kwallo 35.

‘Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Sociedad:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Mendy da kuma Javi Hernández.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma James.

Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...