Hukumomin kwastam dake filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos sun samu nasarar kama wasu jirage marasa matuka da kuma sauran kayayyakin amfani soja da aka yi kokarin fasa kwaurinsu cikin Najeriya.
Mutane uku aka kama da ake zargi suna da hannu a shigo da haramtattun kayan a cewar hukumomin na kwastam.
A cewar kwantirolan yanki na hukumar, Charles Orbih dukkanin jiragen marasa matuki basu da izini daga ofishin mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.