Kwankwaso ya kai ziyara jihar Rivers

[ad_1]
A cigaba da ziyarar tattaunawa da yake da jagororin jam’iyar PDP na kasa baki da daya, tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata a yanzu dake wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Jihar Rivers.

Kwankwaso ya gana da gwamnan jihar,Barrister Nyesom Wike gwamnan da ake gani na daga cikin gwamnonin da suke fada aji cikin jam’iyar PDP.

Sanata Kwankwaso na daga cikin yan takara dake neman jam’iyar PDP ta tsayar takarar shugaban a zaɓen shekarar 2019.

Bayan ganawar da ya yi da Wike Kwankwaso ya kuma tattauna da shugabannin jam’iyar ta PDP na jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayansa.
[ad_2]

More News

Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai...

NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki...

Ƴanbindiga sun kashe mutane a Jihar Kaduna

An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da wasu da dama tare da yin garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka...

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...