Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a jihar Borno ta shafa.
Kwankwaso ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya kewa gwamnan jihar Babagana Umara Zulum jajen ambaliyar ruwan da ta shafi wani sashe na birnin Maiduguri.
Tsohon gwamnan ya jajantawa al’ummar jihar inda ya bayyana alhininsa tare da miƙa saƙon ta’aziyarsa kan mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan.
Da yake ƙarbar tallafin kuɗin a fadar gwamnatin jihar Borno, gwamna Zulum ya godewa Kwankwaso inda ya yi addu’ar Allah ya cigaba da ƙara masa lafiya da yalwar arziki.
A lokacin ziyarar jajen Kwankwaso na tare da shugaban jam’iyar NNPP na ƙasa, Dr. Ahmad Ajuji, Engr Buba Galadima, Hon Abba Kawu Ali, Dr Umar Alkali da kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Tarauni, Mukhtar Umar Yarima.