
Kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa a ranar Asabar ya ziyarci kasar Saudiya domin duba tsarin walwalar da aka shirya alhazan Najeriya da za su yi aikin hajjin shekarar 2025.
Da yake magana a madadin tawagar, Sanata Ali Ndume dake wakiltar mazabar kudancin jihar Borno ya ce sanya idanun kwamitin ya fara ne a Madina inda yan majalisar suka duba abubuwan da suka shafi abinci, wurin zama da kuma sufuri.
Ndume ya ce ziyarar wani bangare ne na nauyin da ya rataya kan majalisar kasa na tabbatar da cewa alhazan Najeriya sun samu kulawar da ta dace lokacin da suke gudanar da aikin hajjin na bana.
“Dukkanin mu mambobi ne na majalisar kasa, mambobin kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa da kuma karamin kwamitin Aikin Hajji,” ya ce.
“Munzo ne domin sanya idanu muga yadda ake kula da alhazai farawa daga nan Madinah,”
Ndume ya ce kwamitin ya tattauna da alhazan da suka fito daga jihar Kebbi wanda su ka sauka jiya kuma sun ya bi masaukin da aka sauke su sosai.
“Sun fada mana babu matsala mun tabbatar an basu karin kumallo akan lokaci kuma abinci mai kyau,” sanatan ya ce.
Ya kara da cewa kwamitin zai cigaba da ziyarar sanya idanu a duk fadin Saudiya domin bibiyar yadda Aikin Hajjin ke tafiya tun daga farawa har a gama.