Daruruwan magoya baya sun hallara a Filin Jirgin Sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi a ranar Alhamis domin tarbar Kwamishinan Kuɗi na jihar, Dokta Yakubu Adamu, bayan dawowarsa daga Abuja.
Kwamishinan ya dawo jihar ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba shi beli a shari’ar da ake tuhumarsa da hannu a zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Magoya bayan, waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na jihar, sun tarbe shi da raye-raye da addu’o’i. Sun bayyana kwarin gwiwa kan cewa ba shi da laifi, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su bar shari’a ta yi halinta.
Da yake jawabi daga baya a gidansu da ke Bauchi, Dokta Yakubu Adamu ya gode wa al’ummar jihar da sauran masu yi masa fatan alheri bisa addu’o’i da goyon bayan da suka nuna masa. Ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da bin doka da oda tare da girmama hukumomi.
Haka kuma, ya roƙi mazauna jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Bala Mohammed baya, yana mai jaddada kudirin gwamnati na hanzarta ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa shari’ar tana nan a gaban Babbar Kotun Tarayya, yayin da ake sa ran Kwamishinan zai ci gaba da bin sharudan belin da aka gindaya masa.
Kwamishinan Kuɗi Na Bauchi Ya Samu Gagarumar Tarba Bayan Samun Belin Kotu

