Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Ta Mayar Wa IPOB Martani

[ad_1]

A cikin wata takardar da ta rabawa manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra, a ranar Laraban da ta gabata, kungiyar IPOB tace idan har kungiyar Ohanaeze Ndigbo na neman zaman lafiya da jituwa da ita, to fa sai ta fito karara ta jagoranci gwamnonin kudu maso gabas, wajen soke haramcin da aka yi wa kungiyar IPOB, saboda sune suka fara haramta kungiyar kafin gwamnatin tarayya ta ayyana ta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda. Ta kuma ce lallai sai kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta matsa wa gwamnatin tarayya lamba ta soke haramcin da ta yi wa kungiyar. Haka zalika, kungiyar IPOB tace wajibi ne gwamnonin yankin da kungiyar Ohanaeze Ndigbo su nemi afuwa daga gareta, akan hada baki wajen zuga atisayen “Operation Python Dance,” da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan membobinta a bara.

Banda wadannan sharrudan, kungiyar IPOB ta kuma bukaci kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta fito a bainar jama’a ta tambayi wurin da shugabanta, Mista Nnamdi Kanu da iyayensa suke, kana ta nemi afuwa daga al’ummar Afaraukwu-Ibeku, garinsu Nnamdi Kanu akan harin da aka kai fadar sarkin garinsu, wato mahaifin Nnamdi Kanu.

Bisa wadannan sharrudan ne wakilin Sashen Hausa Alphonsus Kkoroigwe, ya zanta da Barista Uche Achi Okpaga, sakataren yada labarai na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, inda ya mayar da martini da cewa,

“Idan kungiyar Ohanaeze Ndigbo tana yiwa kungiyar IPOB kallon kungiyar ‘yan ta’adda, bazamu shiga neman wani sulhu da ita ba, saboda ba abin boyewa bane cewa bamu taba musu kallon kungiyar ‘yan ta’adda ba. Yanzu mu fito muce gwamnati ta soke haramcin da ta yi wa kungiyar IPOB bashi da wani amfani saboda tafiyarmu daya ne da tasu, kuma mun sha fadin cewa lakaba wa ‘yan kungiyar sunan ‘yan ta’adda abin Allah wadai ne. Yanzu, akan batun wurin da Nnamdi Kanu da iyayensa suke, mun sha la’antar matakan da aka dauka da suka yi sanadiyar bacewarsu. A ce mu roki afuwa na nufin cewa idan kungiyar Ohanaeze Ndigbo ce ta yi garkuwa dasu, ta dawo dasu. Daga aukuwar wannan lamarin zuwa yanzu, kungiyar Ohanaeze bata daina la’antar bacewarsu ba. Saboda haka, ba a yi mana adalci ba a ce mu fara abin da muka dade muna yi.”

Barista Okpaga ya kara da cewa kungiyar Ohanaeze Ndigbo zata ci gaba da tattaunawa da ‘yan awaren IPOB don samar da kyakkyawar fahimta tsakanin kungiyoyi biyun.

Shi ma a nasa bayanin, babban daraktan kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Farfesa Simon Ortuanya ya bayyana cewa, mutum guda ba zai iya zama ya yanke shawara ko kuma bayyana matsayin gwamnonin yankin kan wannan lamarin ba. Yana mai cewa:

“Mayar da martani akan takardar sanarwa abu ne na gama gari, wanda ya zama dole ne sai gwamnonin sun hadu kafin a yanke shawara. Saboda haka, ba abin mutum guda bane yace zai roki afuwa ko bazai roka ba. Dole ne ya zamana shawarar ta kungiyar ce, ba ta mutum guda ba; wato ta kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, kuma sai sun hallara ne zasu yanke shawarar mayar da martini, idan akwai bukata. Saboda haka, bani da alhakin mayar da martani a madadin gwamnonin kudu maso gabas.”

Bayan taron sulhun da tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo Farfesa Ben Nwabueze ya kira kusan makonni biyun da suka gabata a garinsa Atani dake kusa da Anacha bai yi wani tasiri ba, akwai alamun cewa da sauran aiki a duk yunkurin samar da jituwa tsakanin kungiyar IPOB da kungiyar Ohanaeze Ndigbo da kuma gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...