
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya,CAN ta shawarci gwamnatin tarayya da ta sako jagoran kungiyar Shi’a a Najeriya, Ibrahim Elzakzaky da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro kanal Sambo Dasuki mai ritaya da gwamnatin ke cigaba da tsare su.
Har ila yau kungiyar tayi roko na musamman ga gwamnatin tarayya da tabbatar ta cigaba da tattaunawa kan sakin Leah Sharibu da kuma sauran ragowar yan matan Chibok dake cigaba da zama a hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
CAN ta kuma gargadi malaman coci da su kaucewa kirkirar wasu faloli da abin mamaki da sunan Allah ne ya samar da su inda ta ce hakan ka iya jawo musu fushin Allah.
Shugaban kungiyar ta CAN na kasa baki daya Samson Olasupo Ayokunle shine ya yi wannan kira a wurin wani taron manema labarai gabanin fara taron cocin Baptist dake Najeriya a Ogbomoso cikin karshen mako.