Kungiyar ƙwadago ta NLC ta dage kan tsunduma yajin aiki

Kungiyar ƙwadago ta NLC ta ce babu wata yarjejeniya da ta shiga da gwamnatin tarayya domin ta dakatar da shiga yajin aikin sai baba ta gani da kuma zanga-zanga da ta shirya farawa a ranar 3 ga watan Oktoba.

A ranar Laraba, Olajide Oshundun daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar ƙwadago da ayyukan yi aka jiyo shi yana fadin cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar NLC kan janye kudirin shiga yajin aikin.

A yayin da Oshundun ya musalta faɗin wannan maganar shima sashen yaɗa labarai da hulda da jama’a na kungiyar NLC ya musalta rahoton a cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

Shugaban sashen Benson Upah shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar.

“Bamu da wata yarjejeniya da gwamnati kan janye yajin aikin da aka shirya ko. Ba mu da kuma wata rana da aka saka ta yin taro da gwamnatin tarayya da zai kai ga an janye yajin aikin da aka shirya shiga.” ya ce

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...