
Mambobin kungiyar kwadago ta NLC sun fara gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawarsu da cire tallafin man fetur.
A jihar Lagos masu zanga-zangar sun taru a karkashin gadar Ikeja inda suka fara zanga-zangar.
A can birnin tarayya Abuja an samu rahoton karya kofar shiga harabar majalisar tarayya a lokacin da aka yi kokarin hana yan kungiyar ta NLC shiga ciki.
A makon da ya gabata ne kungiyar ta NLC ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin mako daƴa domin ta janye duk wasu tsare-tsarenta da ke musgunawa talaka.
Zanga-zangar dai ta gudana lafiya a jihohi da ke fadin Najeriya.