
Kungiyar ƙwadago ta NLC ta ce babu wata yarjejeniya da ta shiga da gwamnatin tarayya domin ta dakatar da shiga yajin aikin sai baba ta gani da kuma zanga-zanga da ta shirya farawa a ranar 3 ga watan Oktoba.
A ranar Laraba, Olajide Oshundun daraktan yaÉ—a labarai na ma’aikatar Æ™wadago da ayyukan yi aka jiyo shi yana fadin cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar NLC kan janye kudirin shiga yajin aikin.
A yayin da Oshundun ya musalta faÉ—in wannan maganar shima sashen yaÉ—a labarai da hulda da jama’a na kungiyar NLC ya musalta rahoton a cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
Shugaban sashen Benson Upah shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar.
“Bamu da wata yarjejeniya da gwamnati kan janye yajin aikin da aka shirya ko. Ba mu da kuma wata rana da aka saka ta yin taro da gwamnatin tarayya da zai kai ga an janye yajin aikin da aka shirya shiga.” ya ce