Kun san wanda ya kai hari London ranar Talata?

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Salih Khater

An kama mutumin ne bisa zargin ta’addanci bayan motarsa ta daki wani shinge a wajen majlisar dokokin Birtaniya.

Gabanin motar ta daki shingen, sai da mutumin da ake zargi Salih Khater ya bi ta kan wasu mahaya kekuna dake jiran a basu hannu.

Hukumomi sun ce Salih Khater dan asalin kasar Sudan ne amma haifaffen Birtaniya.

Tuni dai yan sanda suka fara yi masa tambayoyi a kudancin London.

Mutane uku sun ji rauni bayan motar ta kade wasu mahaya kekuna da masu tafiyar kafa da safiyar Talata.

An kai mutane biyu asibiti bayan hadarin kuma an sallame su daga baya.

Salih Khater ba ya cikin mutane da hukumar leken asirin Birtaniy M15 ko yan sandan da ke yaki da ta’addanci suke sa ido a kansu, sai dai ‘yan sandan unguwarsu sun san shi.

Image caption

Lokacin da ‘yan sanda suka kama mutumin da ake zargi da kai harin ke nan.

[ad_2]

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...