Kotun koli ta dakatar da CBN daga daina amfani da tsofaffin takardun Naira

Kotun koli ta dakatar da Babban Bankin Najeriya CBN daga shirin sa na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin Naira a ranar 10 ga watan Faburairu kamar yadda bankin ya tsara.

Jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Kogi su ne suka shigar da kara gaban kotu.

A yayin zamanta na yau kotun ta bayar da umarnin wucin gadi har zuwa ranar 15 ga wata lokacin da za ta cigaba da sauraron karar.

More from this stream

Recomended