Kotun koli ta dage sauraron karar shari’ar sauya kuɗin Naira

Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni suka shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa ranar Laraba mai zuwa.

Gwamnonin Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara ne dai suka garzaya kotun suna neman a hana Babban Bankin Najeriya CBN daina amfani da tsoffin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200 daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.

Kotun dai, a yayin zamanta na ranar Laraba ta dage ci gaba sauraron karar har zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairun 2023.

A yayin zaman kotun na yau an samu karin wasu jihohi da suka nemi a saka su a cikin jerin waɗanda suke kara da kuma wasu jihohin dake neman a saka su bangaren waɗanda ake kara.

More News

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 191 tare da kama 184

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja...

Farashin gangar ɗanyen man fetur ya ƙaru zuwa $97

Farashin ɗanyen man fetur ya karu sosai a ranar Alhamis inda aka rika sayar da kowacce ganga kan dalar Amurka $97. Farashin man nau'in Brent...

Kungiyar ƙwadago ta NLC ta dage kan tsunduma yajin aiki

Kungiyar ƙwadago ta NLC ta ce babu wata yarjejeniya da ta shiga da gwamnatin tarayya domin ta dakatar da shiga yajin aikin sai baba...

Wani wanda ya gama jami’a ya yi yunkurin kashe kansa saboda rashin ba shi satifiket ɗinsa

Wani wanda ya kammala karatun digiri a jami’ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a jihar Edo mai suna Precious Ogbeide ya yi yunkurin kashe...