Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tabbatar da zaɓen Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar Gombe.
Kotun mai alkalai uku dukkansu sun amince cewa jam’iyar PDP da kuma ADC dukkansu sun gaza tabbatar da zargin da suke cewa an saba ka’ida da kuma rashin bin dokokin zaɓe a karar da suka shigar daban-daban a gaban kotun.
Mai shari’a, Orji Abadua wanda ya shine ya karanta hukuncin alkalan ya tabbatar ds hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaɓen gwamna ta yi na korar karar da ɗan takarar jam’iyar PDP Jibrin Barde ya shigar.