Kotun ɗaukaka ta soke zaɓen shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja, ta soke zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman.

Alkalan kotun uku sun bayar da umarni da a sake zaɓe a wasu akwatuna biyar.

A watan Satumba, kotun sauraren kararrakin zaɓe dake Kaduna ta kori Liman inda ta bada umarnin sake a zaɓe a wasu akwatuna 42.

Ɗan takarar jam’iyar PDP, Solomon Katuka shi ne ya shigar da ƙara a gaban kotun kan zaɓen na Mazabar Makera.

Rashin gamsuwa da hukuncin ya saka Liman wanda shi ne ɗan takarar jam’iyar APC ya ɗaukaka ƙara.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta kori ƙarar da ya ɗaukaka inda ta bayar da umarnin sake zaɓen a akwatuna biyar.

Kotun ta yanke hukuncin cewa tazarar kuri’u 382 tsakanin Liman da Katuka ba su kai yawan katin zaɓen da aka karba a akwatunan ba.

More from this stream

Recomended