Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Sokoto

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da zaɓen, Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Rukunin alkalan kotun su uku sun yi watsi da ɗaukaka ƙarar da jam’iyar PDP da ɗan takararta, Saidu Umar suka yi inda suke ƙalubalantar nasarar da Aliyu ya samu.

Dukkanin alkalan uku sun ce ba su ga dalilan da zai sa su yi gyara ga hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan da ya bawa Aliyu nasara ba.

Aliyu da ya yiwa jam’iyar APC takara ya lashe zaɓe da kuri’a 453,661 a yayin da Umar ya samu kuri’a 404, 632.

Amma Umar ya yi zargin cewa gwamnan da mataimakinsa Idris Gobir sun miƙawa hukumar INEC takardun kammala makaranta na jabu domin su samu damar tsayawa takara.

Masu ƙarar sun kuma yi zargin cewa anyi magudi a zaben.

Kotun a hukuncinta na ta tace sun gaza tabbatar da gaskiyar zarge-zarge 6 da suka shigar da kara akansu.

More News

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...

Hoto: Ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu A Ƙasar Qatar

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu na cigaba da ziyarar kwanaki biyu a ƙasar Qatar. A yayin ziyarar Tinubu ya gana sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...