Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen da aka yiwa Usman Ododo a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kogi.
A hukuncin da ta zartar ranar Juma’a rukunin alƙalan kotun su biyar sun yi watsi da ƙarar da jam’iyar SDP da ɗantakararta Murtala Ajaka suka shigar.
Kotun ta ce ɗaukakar da suka yi bashi da tushe bare makama.
Mai shari’a, Sadiq Umar da ya karanta hukuncin ya yi watsi da dukkanin bukatoci uku da masu ƙara suka ɗaukaka ƙara akai.
Har ila yau kotun ɗaukaka ƙarar tayi watsi da ƙarar da jam’iyar AA da ɗantakararta Olayinka Baimoh suka shigar akan nasarar da Ododon ya samu.
Kotun ta kuma umarci mai ƙarar da ya biya naira miliyan biyar ga wanda aka yi ƙara wato gwamna Usman Ododo.