Kotu tayi watsi da bukatar Emefiele da ta nemi EFCC ta dawo masa da gidaje 743

Mai Shari’a, Jude Onwuegbuzie na babbar kotun tarayya dake Abuja ya yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya gabatar gabansa inda ya nemi kotun ta dawo masa da wasu rukunin gidaje guda 743 dake Abuja da hukumar EFCC ta kwace masa.

Rukunin gidajen da aka gina a fuloti mai lamba 109 dake gundumar Lokogoma na girman murabbain 150,462.84.

Tunda farko hukumar EFCC dake yaki da masu  yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta samu umarnin wucin gadi daga kotun kan ta mallakawa gwamnatin tarayya rukunin gidajen.

Duk da cewa da farko EFCC ta bayyana cewa an kwato gidajen ne daga hannun wani tsohon babban jami’in gwamnati Emefiele ta hannun lauyansa ya gabatar da bukata a gaban kotu inda ya nemi shiga magana.

Emefiele ya ce an gudanar da baki dayan batun kwace gidajen ba tare da saninsa ba inda ya yi zargin cewa EFCC ta wallafa bayanin kwacewar a wani sako na jarida da ba a gani sosai abun da ya yi masa wahalar mayar da martani akan lokaci.

More from this stream

Recomended