
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar neman beli da tsohon babban lauyan gwamnatin kuma ministan shari’a a, Abubakar Malami ya gabatar gaban kotu inda ya ke neman hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta sake shi.
Alkalin kotun Mai shari’a, Babangida Hassan ya ce ba zai iya amincewa da bukatar bayar da belin ba saboda wata kotun dake da hurumin sauraren karar ta bawa hukumar EFCC damar cigaba da tsare tsohon ministan domin ta cigaba da bincike.
Tun ranar Litinin ta makon da ya gabata ne Malami ke tsare a hannun hukumar EFCC kan zargin da ake masa na almundahanar kudade.
Malami ya gabatar da bukatar neman belin ne ta hannun lauyansa, Sulaiman Hassan SAN.
Tsohon ministan ya ce cigaba da tsare shi da hukumar take ya saba doka.
Amma kuma lauyan EFCC, Jibrin Okutepa wanda shima yake da mukamin SAN ya gabatar da hujjar cewa EFCC na tsare da Malami sakamakon umarnin da ta samu daga wata babbar kotun tarayya dake Abuja karkashin jagorancin, mai shari’a, S.C Orji

